Bisa labarin da aka samu, an ce, an kama Agbeyome Kodjo wanda a halin yanzu shi ne shugaba na wata jam'iyyar adawa a gidansa da ke birnin Lome, bayan awoyi da dama da aka sanar da kawar da ikon kariyar na hukuncin shari'a a kansa, daga bisani kuma 'yan dokan kasar sun yi masa tambayoyi. Kafin wannan kuma, sun kuma yi wa mataimakin shugaban jam'iyyar bincike bisa wannan dalili.
Ran 10 da 12 ga watan da muke ciki, an samu tashin gobara masu tsanani a kasar Togo har sau biyu, ko da babu wanda ya rasa ransa ko jikkata cikin gobarar, amma, hakan ya haddasa barna mai tsanani. Bayan binciken da rundunar 'yan sandan kasar suka yi, an ce, Agbeyome Kodjo na da hannu cikin wadannan hadarurruka. Shi ya sa, don gudanar da binciken da ake yi, hukumar gurfanar da mutane a kotu ta kasar ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta kawar da ikon kariya na hukuncin shari'a na Agbeyome Kodjo.
Agbeyome Kodjo shi ke matsayin shugaban majalisar dokokin kasar Togo tsakanin shekarar 1999 da ta 2000. Ko da ya sauka daga matsayin a shekara ta 2000, yana ci gaba da samun kariyar iko na hukuncin shari'a na mambobin majalisar dokokin kasar. (Maryam)