A cikin jawabin fatan alheri da ya yi, Mr. Feng ya ce, a cikin shekaru 40 da suka shude, wato bayan da kasashen Sin da Togo suka kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, duk da sauyawar yanayin siyasa da ake fuskanta a duniya, dangantakar bangarorin biyu ta ci gaba da habaka lami lafiya, a karkashin goyon baya da kulawa daga shugabannin kasashen biyu, bangarorin biyu na kara yin mu'amala cikin aminci, kuma mu'amalar al'adu ta ci gaba da habaka tsakaninsu, kana an samu sakamako mai gamsarwa wajen yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu.
Jakadan kasar Togo da ke kasar Sin Nolana Ta Ama ya ce, Togo ta nuna goyon baya ga kasar Sin, kuma an kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu ne bisa amincewar da aka samu ta fuskar siyasa cikin daidaito, da cimma moriyar juna cikin nasara a fannin tattalin arziki, da mu'amalar al'adu a tsakaninsu. Ofishin jakadancin Togo da ke kasar Sin yana fatan ci gaba da fadada dangantakar sada zumunta da ke tsakanin kasashen biyu, domin dorewar hadin gwiwa tsakaninsu a dukkan fannoni.(Bako)