Wang Min wanda shi ne mataimakin wakilin kasar Sin a MDD, ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD a ranar Alhamis cewa, kasar Sin tana fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa, za su nuna dattaku da sanin-ya-kamata, aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma bil-hakki da gaskiya, warware bakin dayan tashin hankali da takaddamar da ke faruwa a shiyyar, kana su fara yunkurin shimfida zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Ya ce, nauyin da ke gaban bangarorin a halin yanzu, shi ne gaggauta tsagaita bude wuta tare da maido da zaman lafiya a gabashin Jamhuriyar demokiradiyar Congo(DCR). Inda ya yi kira ga kungiyoyin da ke dauke da makamai da su cimma yarjejeniya da gwamnatin DRC dangane da kawo karshen tashin hankali a kasar. (Ibrahim)