in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nada mai bada shawara na musammam ga yankin Great Lakes
2013-04-30 16:50:31 cri

A ranar Litinin 29 ga wata ne, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya nada Modibo Toure, wani dan kasar Mali a matsayin mai bada shawara na musamman ga manzon musamman na babban sakataren MDD kan yankunan Great Lakes.

A cikin wata sanarwar da kakakin Ban Ki-moon ya bayar, ya bayyana cewa, a matsayinsa na mai bayar da shawara na musamman da ke da zama a Kenya, Mr Toure zai yi aiki ne kafada da kafada da Mary Robinson, manzon musamman ta babban sakataren MDD game da yankunan Great Lakes.

A cewar sanarwar kafin a nada shi bisa wannan mukami, Toure yana aiki ne tun watan Janairu a matsayin wakilin MDD kuma jami'in gudanarwar harkokin bil-adama kana wakilin shirin raya kasashe na MDD mai kula da Kenya.

Sanarwar ta ce, bisa ga wannan mukami, Toure zai rika taimakawa kokarin Madam Robinson na samar da zaman lafiya, tsaro da hadin kai a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da kuma shiyyar baki daya.

A ranar 24 ga watan Fabrairu ne kasashe 11 da ke yankin Great Lakes suka sanya hannu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, kan yarjejeniyar inganta halin da ake ciki a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, yanzu ke nan Mr. Toure yana da kwarewar aiki na shekaru 22 a bangaren ci gaban tattalin arziki na kasa da kasa, inda ya yi aiki da kasashe dabam-dabam da ke gudanar da shirin raya kasashe na MDD(UNDP) a Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China