Rhoda Kaisho, babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Uganda ya shaida wa manema labaru cewa, a yayin taron da za a yi kwanaki biyu ana gudanarwa daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Disamba, za a shigar da sabuwar jamhuriyar Sudan ta Kudu a matsayin mamba a kungiyar, wadda ke taimaka wajen samar da zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali da bunkasuwa a wannan yanki.
Nathan Byamukama, wani jami'in kungiyar ta ICGLR ya ce, shigar da Sudan ta Kudu din a kungiyar zai taimaka wajen kawo karshen rikice-rikice da rashin tsaro a yankin.
Ana sa ran shugabannin kasashe goma sha daya ne za su halarci taron, wadanda suka hadar da Angola, Burundi, Afirka ta Tsakiya, Congo(Kinshasa), Congo(Brazzaville), Kenya, Rwanda, Sudan, Uganda, Tanzania da Zambia, inda za a tattauna kan kalubalen da yankin ke fuskanta na rikice-rikicen da ke tsakanin maza da mata.
Kazalika Sudan ta Kudu ta nemi shiga kungiyar kawancen kasashen gabashin Afrika, wadda ta kunshi da Uganda, Kenya, Tanzania, Rwanda da Burundi.(SALAMATU)