Wata sanarwa da UNOCA ta bayar a ranar Talata yayin taron kolin shiyyar da ake gudanarwa da nufin dakatar da fadan da ke faruwa a gabashin jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC), ta bayyana cewa, za a mayar da hankali ne kan bangarorin zaman lafiya, tsaro, hana abkuwa da kuma daidaita rikici.
Wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da yankin Afirka ta tsakiya Abou Moussa, ya ce hadin gwiwa da ICGLR ya zama wajibi, domin yin hakan na taimakawa wajen bayyana yunkurin MDD na goyon bayan shiyyar da kungiyoyin da ke yankin a kokarin da suke na tunkarar kalubalen da ke barazana ga zaman lafiyan kasa da kasa.
Babban sakataren ICGLR Daniel Alphonse Ntumba Luaba Lumu, shi ne ya sanya hannu a madadin kungiyar wadda da hallara kan kasashe 11 wadanda suka hada da Angola, Burundi, Jamhuriyar Afurka ta tsakiya, Jamhuriyar Congo, Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Kenya, Uganda, Rwanda, Sudan, Tanzanina da kuma Zambia.
Sanarwar ta ce, hadin gwiwa tsakanin UNOCA da ICGLR zai mayar da hankali ne kan wasu batutuwa tsakanin sassan biyu, wadanda suka hada da bayar da goyon baya wajen shiga tsakani, shugabanci da manufofin tsaro, baiwa mata kwarin gwiwar shiga harkokin hana abkuwa da daidaita rikici. (Ibrahim Yaya)