Kasashen dake gabar manyan tafkunan Afrika na kokarin kulla dangantaka ta fuskar makamashi da aikin gona
A ranar Litinin da ta gabata ministocin harkokin waje na kasashen Burundi, Ruwanda da jamhuriyyar demokradiyyar Congo wanda suka samar da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen dake gabar manyan tafkunan Afrika (CEPGL), suka fara gudanar da wani taro na tsawon kwanaki biyu a Bujumbura, babban birnin kasar Burundi, domin lalubo hanyoyin bunkasa sha`anin makamashi, kayayyakin more rayuwa da kuma ayyukan gona a tsakaninsu.
Ministan harkokin waje na kasar Burundi Augustine Nsanze wanda ya bude zaman taron, ya bayyana irin muhimmancin da taron yake da shi wajen sake dawo da hadin kan kasashen yankin wanda ya samu matsala tun a 2007.
Ya ce taron zai amince da shawarwarin da kwararru suka bayar yayin taron da suka gudanar.
Da yake magana, sakataren kungiyar Herman Tuyaga ya tabbatar da cewa, mahalarta taron za su gano hanyoyin habaka sha`anin makamashi, aikin gona, samar da kayayyakin more rayuwa da kuma harkar samar da abinci a yankin. (Bagwai)