in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda ya zargi kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da nuna kaskanci ga Afirka
2011-12-17 17:30:59 cri
A ranar Juma'ar nan, shugaba Yoweri Museveni na Kasar Uganda, ya zargi kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC), da nuna wariya ga Afirka, yana mai cewa, akwai manyan makirce-makirce da aka tafka a wasu wurare a duniya, amma ba a hukunta wadanda suka aikata su ba.

Museveni, wanda shi ne shugaban taron kasa da kasa na yankin manya tafki (ICGLR), wata kungiyar da take hada kan kasashe 11, ya shedawa manema labarai cewa, yayin da Afirka take goyon bayan kafuwar kotun, irin yadda ake ganin tana nunawa Afirka rashin adalci na jawo matsaloli.

Ana dai tattaunawa ne kan nasarorin da aka samu ta fuskar tsaro, bunkasa da yawan kalubalen da yankin ke fuskanta ne a zaman taron.

Shugabannin wasu kasashe mambobin wannan kungiya ta ICGLR, suna fuskantar tuhuma daga kotun ICC, wacce take zarginsu da aikata laifukan yaki da manyan laifukan kan al'ummunsu.

A cikin watan Yulin bana ne kungiyar tarayyar Afirka AU, ta yanke shawarar daina baiwa kotun hadin kai, bayan zargin ta da nuna wariya, gami da yin zabe a cikin harkokinta na shari'a. (Garba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China