in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya gamsu da yarjejeniyar da Sudan da Sudan ta kudu suka kulla
2012-09-29 10:23:21 cri
Ranar 28 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi jinjina ga yarjejeniyar da Sudan da Sudan ta kudu suka kulla, kuma ya ce, wannan ya kasance muhimmin mataki ne ga samar da zaman lafiya da wadata a kasashen biyu.

Sanarwar ta ce, kwamitin ya gamsu da karfin jagorancin da shugabanni da wadanda suka shiga shawawari wajen fitar da matakin warware rikici mai kyau tsakanin kasashen biyu. Ci gaba da aka samu ba ma kawai zai samar da zaman lafiya, wadata a kasashen, har ma zai kawo makoma mai haske ga jama'ar kasashen biyu wajen tabbatar da zaman lafiya cikin dogon lokaci da sada zumunci tsakaninsu.

Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, kwamitin ya jaddada wajibcin tabbatar da yarjejeniyar nan da nan, da kuma bukatar bangarorin da abin ya shafa da su ci gaba da taka rawarsu domin warware wasu batutuwa dake kan tebur, musamman ma batun matsayin yankin Abyei dake jawo hankalinsu sosai.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China