A wannan rana, a Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, mista Mbeki ya gaya wa kafofin yada labaru cewa, yarjejeniyar da bangarorin 2 suka cimma ta shafi dukkan batutuwan man fetur, ciki har da matsalar kudin da za a kashe kan yin jigilar man fetur, sarrafa shi da yin jigilar shi tsakanin kasashen 2 ba a warware ta ba. Ya kara da cewa, Sudan ta Kudu za ta maido da hakowa da kuma sayar da man fetur zuwa kasashen ketare.
Duk da haka mista Mbeki bai yi wani bayani sosai ba, sa'an nan kuma, kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ba su bayyana kome ba kan lamarin.(Tasallah)