A cikin sanarwar bayan taron hadin gwiwa na kwanaki biyu, jiko na shida tsakanin Afirka ta kudu da kungiyar EU wanda aka yi a birnin Pretoria, an yi kira ga bangarori uku na yarjejeniyar siyasa da su tabbatar sun dauki dukkan matakai da suka dace don tabbatar da ganin an gudanar da zaben cikin kyakyawan yanayi na lumana kuma ba tare da magudi ba domin a samu cimma sakamako da zai nuna a zahiri zabin jama'ar kasar Zimbabwe.
A yayin taron, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi dangane da kasar Zimbabwe da kuma kan batun zaben kasar da za'a yi ran 31 ga watan Yuli.
Sanarwar bayan taron na mai ci gaba da cewa suna maraba da bullo da sabuwar doka a kasar da kuma nuna goyon baya ga shigowar kungiyar bunkasa al'ummar kudancin Afirka (SADC) da kungiyar hadin kan kasashen Afirka (AU) cikin batun, musamman ma a fuskar sa ido kan zaben, inda hakan zai tabbatar da gudanar da zaben ba tare da magudi ba kuma cikin lumana. (Lami Ali)