A ranar Alhamis, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya taya tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Phumzile Mlambo-Ngcuka murna game da matsayin da ta samu a MDD.
A ranar Laraba, magatakardan MDD, Ban Ki-Moon ya baiwa Mlambo Ngcuka matsayin babbar darektar cibiyar yancin jinsi da daukaka matsayin mata ta MDD.
Cikin wata sanarwa, Zuma ya ce, 'A madadin gwamnati da daukacin jama'ar Afirka ta Kudu, ina taya tsohuwar mataimakiyar shugaban kasa murna kan wannan muhimmin matsayi.'
Mlambo Ngcuka ita ce mataimakiyar shugaban kasar Afirka ta Kudu daga shekarar 2005 zuwa ta 2008, inda ita ce mace ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban kasa a kasar.
Da kuma yake yabon Mlambo Ngcuka kan wannan ci gaba, shugaba Zuma ya ce, ko shakka babu wannan matsayi tamkar wani yabo ne kan gudummawa da take bayarwa a fuskar daukaka matsayin mata a Afirka ta Kudu da kuma nuna gamsuwa kan irin rawa da kasar Afirka ta Kudu da jama'arta ke takawa a fagen kawo ci gaba a duniya. (Lami)