Kakakin MDD Martin Nesirky ya bayyana wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, mataimakiyar babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai Valerie Amos ta yi kiran da a kara samarwa jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR kayayyakin jin kai, yayin da kasar ke ci gaba da fama da rashin tsaro da matsalar abinci.
Martin Nesirky ya bayyana hakan ne a Bangui, babban birnin kasar, inda ya bayyana matukar damuwa game da rokon da al'ummomin da tashin hankali ya shata a sassa daban-daban na kasar, inda ya yi kiran da a kara samar da kayayyakin jin kai da jama'a ke bukata cikin gaggauwa.
Amos ta ce, rikicin ya shafi baki dayan al'ummar kasar miliyan 4.6, kana ta bayyana matukar damuwa kan yadda tashin hankalin ya fi shafar mata da kananan yara.
Bugu da kari, kakakin na MDD ya ruwaito jami'ar na cewa, babbar damuwar ita ce matsalar tsaro, kuma MDD tana aiki ba dare ba rana don ganin ta sake bullo da matakai gami da wasu shirye-shirye a sassa daban-daban na kasar. (Ibrahim)