Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ran 13 ga wata, sabbin kudi da wani kamfanin kasar Britaniya ya buga ya isa bankin tsakiyar jamhuriyar Sudan ta Kudu, kuma za a kaddamar da shi a ran 18 ga wata. Daga cikinsu akwai iri-irin Fam 1, Fam 5, Fam 25, Fam 50 da Fam 100.
Ban da haka kuma, bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin kasar ta buga sabon fasfo, ko wane dan kasar zai iya samun sabon fasfo idan ana son yin tafiye tafiye ko yawon shakatawa a kasashen waje.(Abubakar)