in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kara wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke Sudan ta Kudu
2013-07-12 10:23:43 cri

A ranar Alhamis ne kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri'ar amincewa da kara wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke aiki a Sudan ta kudu (UNMISS) zuwa ranar 15 ga watan Yulin shekara ta 2014, kana ya yi Allah-wadai da tashin hankalin da ke faruwa a kan iyakar tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

A cikin wani kudurin da kwamitin sulhun ya amince da shi, kwamitin ya yi maraba da kafa hukomomi da majalisun dokokin da gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi, da rage karuwar rikici da tashin hankali, musamman a jihar Jonglei, inda fadan da ake tsakanin dakarun Sudan ta Kudu da kungiyoyi masu dauke da makamai a Jonglei, ya raba dubban mutane da gidajensu, yayin da kuma 'yan bindiga suka halaka ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD guda 5 da wasu ma'aikata fararen hula 7, a wani kwanton bauna da suka yi musu a watan Afrilu.

Kwamitin sulhun ya yi kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su hanzarta tsagaita bude wuta da daina keta hakkin bil-adama, musamman kan mata da kananan yara.

Bugu da kari, kwamitin ya nuna bacin ransa matuka kan yadda al'amuran jin kai suka tabarbare sakamakon fadan kabilanci da kuma yadda aka takaita zirga-zirgar tawagar UNMISS.

Daga karshe, kwamitin ya kuma yi kira ga gwamnatin Sudan ta Kudu da ta dauki matakan da suka wajaba tare da kara hada kai da tawagar UNMISS don kare fafaren hula, aiwatar da shirin kwance damarar makamai da janye dakarunta daga dukkan fannoni. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China