Bisa labarin da aka bayar, an ce, kwanan baya, ma'aikatar kula da harkokin man fetur ta Sudan da ta Sudan ta Kudu, sun ba da umurnin farfado da hadin gwiwa game da man fetur tsakanin bangarorin biyu, da batun fitar da shi zuwa kasashen waje. Hong Lei ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labaru game da wannan batu. Ya ce, kasar Sin tana ganin cewa, bangarorin biyu, za su kyautata dangantaka a tsakaninsu, da inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, tare da kuma fatan bangarorin biyu, za su cika alkawarin da suka dauka, don warware sauran batutuwa ta hanyar shawarwari bisa wannan tushe.(Bako)