in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Botswana ya bukaci gwamnatocin Afrika dasu kyautata tsarin aikin ma'aikatun gwamnati
2013-07-24 13:49:51 cri
Mataimakin shugaban kasar Botswana Ponatshego Kedikilwe ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su kara kyautata tsarin aikin ma'aikatun gwamnati ta hanyar kawo armashin zama tsakanin 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati, ta yadda za'a cimma wani cigaba mai karko a nahiyar Afrika.

A yayin da yake jawabi a gaban wakilan dandali karo na 10 na shugabannin ma'aikatun gwamnatin kasashen Afrika mambobin kungiyar Commonwealth, mista Kedikilwe ya bayyana cewa nahiyar Afrika na cigaba da rasa lokaci kan kokarinta na cimma cigaba mai karko. Hakazalika yayi kira wajen kafa hulda mai kyau tsakanin 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati, ta wannan hanya ce kadai za'a kawo armashin zama.

Dandalin dake gudana ya samu halartar shugabannin ma'aikatun gwamnatocin kasashen Botswana, Kamaru, Gambia, Ghana, Kenya, Lesotho, Malawi, Maurice, Mozambique, Namibia, Nijeriya, Rwanda, Seychelles, Sierra Leone, Afrika ta Kudu, Swaziland, Tanzania, Uganda da Zambia. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China