in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNCTAD ta baiwa kasashen Afirka shawarar karfafa harkar cinikayya a nahiyar
2013-07-12 16:47:41 cri
Taron MDD kan cinikayya da cigaba (UNCTAD) ya bayar da wani rahoto game da bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar Afrika a shekarar 2013 a ranar Alhamis a hedkwatarsa dake birnin Geneva na kasar Switzerland, inda ya baiwa kasashen Afrika shawarar karfafa harkar cinikayya tsakaninsu, tare da kara wa sassa masu zaman kansu kwarin gwiwa, ta yadda za a bunkasa tattalin arzikin Afrika a dukkan fannoni.

Wani abin da aka mai da hankali a kai cikin rahoton shi ne yadda za a karfafa harkar cinikayya tsakanin sassan Afrika, inda ya yi nuni cewa, yawan kason da aka samu a bangaren harkar cinikaya a tsakanin kasashen Afirka bisa na dukkan nahiyar ya ragu wato daga kashi 22.4 cikin dari a shekarar 1997, zuwa kashi 11. 3 cikin dari a shekarar 2011, wanda ya yi kasa da sauran yankunan duniya. Babban sakataren UNCTAD, Supachai ya bayyana a Geneva cewa, kamata ya yi a daga wannan adadin. Ya ce,

"An fitar da wannan rahoton ne da nufin amsa tambayar da ke kan dalilin da ke sanya yawan kudin da aka samu wajen harkar cinikayya a tsakanin kasashen Afrika bai kai matsayin na Asiya da Latin Amurka ba? Yawan cinikayya da ke tsakanin kasashen Asiya ya kai kimanin kashi 50 cikin dari bisa na yawan cinikayyar da kasashen nahiyar suke gudanar a duniya baki daya. Amma, bisa wannan rahoton, yawan kudin da ke tsakanin kasashen Afrika, ya kai kashi 11.3 cikin 100, don haka kamata ya yi adadin ya karu. Wannan na nuna cewa, akwai makoma mai kyau a harkar cinikayya tsakanin sassan Afrika a nan gaba."

Bugu da kari, rahoton ya ce, shugabannin kasashen Afrika baki daya sun tsaida kuduri a watan Janairu na shekarar 2012 na rage shingaye a harkar cinikayya tsakanin shiyyoyin Afrika, don inganta cinikayya a tsakaninsu, ingantattun matakan da ya kamata a nuna yabo a kai. Amma idan gwamnatocin ba su yi kokarin kara yawan irin kayayyakin da suke samarwa, tare da karfafa ingancinsu ba, zai yi wuya a cimma burin inganta cinikayya tsakanin shiyyoyin Afrika. Mista Supachai ya bayyana cewa, muhimman matakan da nahiyar Afirka za ta dauka wajen inganta tattalin arzikinta su ne, kara karfinta na samar da kayayyaki, da na takara:

"Yawan kudin cinikin da aka samu a bangaren masana'antun kirkire-kirkire tsakanin shiyoyyin Afrika kashi 43 cikin dari ne kawai, yayin da a nahiyar Asiya ya kai kashi 65, wannan ya nuna cewa, masana'antun kirkire-kirkire suna da makoma mai kyau ta fuskar ciyar da cinikayya tsakanin shiyyoyin Afirka gaba. Amma, gaskiyar magana ita ce a yanzu haka ana fuskantar wasu matsaloli a sashen masana'antun kirkire-kirkiren Afrika, inda kamfanoni ba sa ci gaba, da gazawar na'urori."

Haka zalika, rahoton na ganin cewa, yanzu gwamnatoci ne kawai ke iya inganta dunkulewar harkar cinikayya ta nahiyar Afrika, yayin da ala tilas sassa masu zaman kansu ke fadi tashi. A wannan yanayin da ake ciki, akwai bukatar a kafa tsarin tattaunawa tsakanin gwamnatocin kasa da sassa masu zaman kansu, inda ya ba da misalin cewa, kasar Mauritius ta kafa wata hukumar daidaito ta masu zaman kansu, don tattaunawa tare da gwamnatin kasar kan manufofin tattalin arziki lokaci lokaci. Game da wannan, mista Supachai ya nuna yabo ga amfanin wannan tsarin tattaunawa, ya ce,

"Ga fasahohin da Asiya ta samu, mun gano cewa, akwai bukatar a kara yin cudanya tsakanin gwamnatoci da sassa masu zaman kansu na kasashen Afrika. Saboda sassa masu zaman kansu na da muhimmanci wajen inganta bunkasuwar cinikayya, su ne kuma za su inganta yunkurin dunkulewar nahiyar Afrika. Don haka kamata ya yi gwamnatoci da sassa masu zaman kansu su yi mu'amala da kara fahimtar juna."

Bayan haka kuma, rahoton ya nuna cewa, tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a kasashen Afrika yana da muhimmanci sosai, kana wani muhimmin mataki ne na bunkasa sassa masu zaman kansu, da ciyar da harkar cinikayya tsakanin shiyoyyin Afrika gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China