in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban sashen kula da harkokin Afrika na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya yi bayyani kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika
2013-07-17 15:59:42 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Tanzaniya da jami'ar Dares Salaam a cikin hadin gwiwa sun shirya taron tattaunawa domin cimma burin raya kasashen biyu, tsakanin ran 15 zuwa 16 ga wata.

Babban sakatare mai kula da harkokin ci gaba dagane da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, kana shugaban sashen kula da harkokin Afrika na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mr Lu Shaye a gun bikin bude taron ya nuna cewa, Sin za ta ba da gudunmawa gwargadon karfinta wajen raya da farfado da nahiyar Afrika cikin lumana.

Wakilin CRI: Yanzu, a cikin wadannen bangarori ne da Sin da Afrika za su yi hadin gwiwa domin cimma burinsu gaba daya?

Lu Shaye: A ganina, da farko, bangarorin biyu za su iya kara tuntubar juna a fannin fasahohin gudanar da ayyukan kasa. Saboda suna da bukatu da muradi gaba daya, don haka ya kamata su kara yin mu'ammala tsakaninsu. Alal misali, Sin ta samu nasara sosai a fannin tattalin arziki a cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata tun lokacin da aka gabatar da manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, kasashen Afrika na fatan koyon fasaha daga kasarmu, hakan ya sa, kasashen Afrika da dama sun dauki matakin koyon fasahar kasar Sin, Sin kuwa na fatan koyarwa kasashen Afrika da basira da ilmi. Saboda haka, kasashen Afrika za su yanke shawara bisa bukatunsu kan yadda za su yi amfani da fasahohin kasar Sin. A sa'i daya kuma, ina ganin cewa, Sin da Afrika na da tunani irin daya a wasu fannoni, kamar dukkanmu mun ki yarda da tsoma baki da wasu kasashen yamma suke yi, da kuma kin yarda da taimakon da wasu kasashen yamma suke bayarwa bisa sharuda da sauransu. Hakan ya sa, ya kamata Sin da Afrika su hada kai domin kafa wani matsayi irin daya a wannan fanni. Sa'an nan, ya kamata Sin da Afrika su kara hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni daban-daban. A shekarun baya, bangarorin biyu sun cimma nasara sosai sakamakon hadin kai, abin da ya samar da basira da ilmi sosai, alal misali a fannin gina manyan ababen more rayuwa, ciniki da tattalin arziki da sauransu. Har wa yau, kasashen Afrika na fatan bunkasa sana'ar kere-kere, masana'antu da sha'anin gona domin neman samun bunkasuwar al'umma, Sin na fatan taimakawa kasashen Afrika wajen tabbatar da burinsu ta hanyar hadin kai.

Wakilin CRI: Ko Sin da Afrika za su fuskanci wasu sabbin matsaloli yayin da suke kokarin cimma burinsu tare?

Lu Shaye: Gaskiya ne. Za mu fuskanci wasu matsaloli yayin da muka cimma nasara. Saboda mu habaka hadin gwiwa tsakaninmu a fannonin daban-daban idan aka kwatanta da can baya, ya kamata mu mai da hankali kan wasu matsaloli tare da magance su tare, ta yadda za mu yi hadin kai yadda ya kamata. Ban da haka, a ganina, ya kamata bangarorin biyu su ba da gudunmawa a wannan fanni. Sin kamata ya yi ta ba da ilmi da jagoranci ga kamfannoni da jama'armu, ta yadda za su yi hadin kai da kasashen Afrika bisa adalci da daidaici da kuma cimma moriya tare. Dadin dadawa, muna fatan kasashen Afrika su ba da jagoranci ga kafofin yada labaru, domin daidaita matsalolin da za su fuskanta dangane da kasar Sin, kuma gwamnatin kasar Sin za ta ba da taimako yadda ya kamata domin daidaita wadannan matsaloli.

Wakilin CRI: Ko wajabi ne bangarorin biyu su yi hadin kai domin tinkarar wasu jita-jita da za su fuskanta?

Lu Shaye: Wannan ya zama wajibi. A ganina, yanzu Sin da Afrika sun samu ci gaba mai kyau, wannan ba abin da ko wace kasa take so ba. Wasu kasashe suna tsoma baki kan hadin kai da Sin da Afrika suke yi bisa nasu bukatar, har ma sun shafa wa kasar Sin bakin fenti a wannan fanni. Game da wannan batu, a ganina, ya kamata bangarorin biyu sun kara kwarin gwiwa da lashe takobin yin hadin gwiwa tsakaninsu duk da zage-zage da ake yi, ban da haka, ya kamata mu mayar da martani kan wasu jita-jita da aka yi.

Masu sauraro, wannan shi ne hirar da wakilinmu ya yi da Mr Lu Shaye kan batun hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China