Shugaban ya fadi hakan ne a Niamey, babban birnin kasar a lokacin kaddamar da wani kwamiti na tattalin arziki,walwalan jama'a da al'adu.
Dangane da batun yin garkuwa da ma'aikata 6 da ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta mai suna kyuatata rayuwan mata da yara na kasar Nijar da wassu masu dauke da makamai suka yi a ranar 14 ga watan nan, shugaba Issoufou ya ce, "za su yi iyakacin kokarinsu na sauke nauyin dake rataye a wuyansu kuma al'ummarsu za su bada gudumuwa yadda ya kamata don taimaka wa jami'an tsaro wajen cigaba da gudanar da ayyukuansu na tsaron yankunan kasar ".
Ya kara da cewa, "mutanenmu ya kamata su gane fuskokin makiyanmu ba tare da shakku ba, wanda duk yake neman kunyata addininmu ta hanyar karya dokokin addinin da kuma sata da shan miyagun kwayoyi makiyinmu ne. Kuma wanda duk yake rayuwa ta hanyar sana'ar yin garkuwa da mutane shi ma makiyinmu ne."
Ya tabbatar da cewa, jami'an tsaro na nan suna binciken yankin gaba daya wanda yake kusa da kan iyaka da kasar Mali don gano mutanen da aka bada rahoton sace su tare da kuma cafke wadanda suka aikata laifin.(Fatimah Jibril)