Mai ba da umurni ga sojojin ya ce, a ran 17 ga wata da dare, sojojin sun kai wani samame wanda ya cimma nasara wajen ceto wadannan mutanen da suka hada da 'yan kasar Faransa biyu, 'yan kasar Amurka biyu, 'yan kasar Indonesiya biyu, da wani dan kasar Canada tare da 'yan kasar Nijeriya 12.
Wadannan mutanen waje 7 an yi garkuwa da su a ran 7 ga wata, a wata rijiyar hakar man fetur a teku na jihar Akwa Ibom dake kudu maso gabashin kasar, kuma wasu 'yan Nijeriya 8 ma an yi garkuwa da su a ran 14 ga wata da dare a wata tashar hakar man fetur a teku dake jihar Akwa Ibom. Kungiyar dauke da makamai mafi girma a kasar wato MEND a jihar Niger Delta ta dauki alhakin wadannan al'amuran 2, kuma ta bayyana niyyar kara kai hare-hare kan wasu na'urorin man fetur. Dadin dadawa, sauran 'yan Nijeriya 4 da aka yi garkuwa da su ma'aikata ne daga wani kamfanin gine-gine na kasar Jamus.(Amina)