Ranar Alhamis 13 ga wata a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake arewacin kasar Kenya wurin dake kusa da iyakar kasar Somaliya, an yi garkuwa da ma'aikatan bayar da agajin na kungiyar likitocin kasa da kasa wato kungiyar Doctors Without Borders.
Jami'in kungiyar ya tabbatar da wannan labari, kuma kungiyar ta kafa wani rukunin magance matsala cikin lokaci domin bincike kan lamarin. Ban da wannan kuma, 'yan sandan wuri sun kafa kangiya a kan iyakar kasa domin cafke masu aikata laifi.
Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya data sanar da daukar alhakin aiwatar da lamarin, amma 'yan sanda suna tuhumar mambobin rundunar adawa da gwamantin kasar Somaliya da hannu a wannan lamari.
A wannan rana da dare, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Spaniya ta ba da sanarwa cewa, mutane biyu da aka yi garkuwa dasu 'yan asalin kasar Spaniya ne, kuma ya ce, kasar za ta yi iyakacin kokari domin ceto wadannan mutane biyu cikin lumana.
Babban jami'in hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD ya yi Allah wadai da lamarin tare da yin kira ga bangarori daban-daban da su taka rawar data dace domin tabbatar kare lafiyar mutanen biyu.(Amina)