in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki ma'aikata 'yan kasar Sudan 11 da aka yi garkuwa da su
2013-01-28 12:19:15 cri

Bisa labarin da wata jaridar kasar Sudan ta bayar a ran 27 ga wata an ce, a ranar 26 ga watan nan ne aka saki ma'aikata 'yan kasar Sudan guda 11, da suka hada da injiniyoyi, da ma'aikata, tare da Sinawa 4 da aka yi garkuwa da su tun ran 12 ga watan nan, a wurin aikin shimfida"Hanyar mota don ceton yammacin kasar"dake jihar Darfur ta arewa ta kasar Sudan, kuma wadannan ma'aikata suna lafiya kalau.

An ce, an saki wadannan mutane ne a wani wuri mai nisan kilomita 17 daga kudu maso yammacin birnin Al Fashir. Mohamed Suleiman Rabih, Shugaban wata gunduma na wannan jihar da iyalan wadannan ma'aikata sun je wurin don taryen su cikin farin ciki. Mohamed ya ce, an saki wadannan mutane ne bisa kokarin da gwamnatin jihar ta yi cikin makwanni biyu, sai dai bai fayyace matakan da aka bi, da sharudan da wadanda 'yan ta'adda suka gabatar kafin sakin mutane ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China