Qiu Xuejun, jagoran tawagar na mutum shida ya sheda ma kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua cewa zasu bada taimako ne ga ofishin jakadancin kasar Sin wajen kokarin ceto wadannan Sinawa tare kuma da yin tattaunawa da Jami'an kasar sudan.
Yace gwamnatin kasar Sin ta damu sosai game da halin da wadannan ma'aikata sinawan ke ciki don haka an shirya wani nau'i na taimakon gaggawa don ceto wadannan ma'aikata.
Kungiyar 'yan adawa da gwamnati ta SPLA wato sudan peoples liberation army ta arewacin kasar a ranar Asabar din da ta gabata suka kai farmaki a harabar da ma'aikatan sinawa ke aiki,kuma mai Magana da yawun kungiyar ranar lahadi ya tabbatar da cewa suna rike da sinawa 29 garkuwa.(Fatimah)