Bisa labarin da aka samu, ya zuwa yanzu, an riga an sayar da jiragen saman Xinzhou kirar 60/600 sama da dari biyu, kuma sha biyar daga cikinsu na amfani da su a kasar Sin, sauran a wasu kasashen Asiya, Afirka da kuma Latin Amurka.
Wani jami'in kamfanin masana'antun jiragen saman kasar Sin ya bayyana cewa, jiragen sama samfurin Xinzhou da kasar Sin ta kera da kanta na samun karbuwa a wasu kasuwannin zirga-zirgar jiragen sama na gajeren zango a duniya. (Maryam)