Wannan gurbatar muhalli abu ne da aka tabbatar a Afirka ta kudu ta fannin ingancin iska da ruwa, yanayin dabbobi da gandun daji, da kuma ta bangaren hanyoyin noma da kiwo, kamar yadda alamun gudanarwa ta fannin bunkasar muhalli a shekara ta 2012 suka nuna.Wannan bincike ya gudana ne a karkashin jami'ar Yale da ta Columbia da ke kasar Amurka tare da hadin gwiwar hukumar kula da tattalin arziki ta duniya.
Gurbacewar muhalli a kasar Afirka ta kudu ta gudana a gaggauce fiye da a cikin sauren kasashen duniya, kamar yadda mujallar kasar da ake kiran Beeld ta sanar. A cikin kasashe 132 na duniya da aka gudanar da binciken kimiyya a kansu danganne da gurbatar muhalli, kasar Afrika ta kudu ta kasance kasar ta 128, a yayin da kasar Iraki ta kasance kutal.(Abdou Halilou).