Ruwan sama kamar da bakin kwarya sun haddasa bala'u masu tsanani a wurare da dama na kasar Sin
Tun lokacin da aka shiga yanayin damina a kasar Sin, an yi ta samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu wuraren kasar, lamarin da ya janyo batsewar wasu kogunan kasar zuwa wani matsayi na wuce kima, birane da dama na fama da ambaliyar ruwa masu tsanani, a wasu wurare kuma an yi ambaliyar ruwa daga tsaunuka, da gangarowar duwatsu da laka, da zabtarewar kasa da dai sauransu, wadanda suka haddasa asarar rayuka da raunata jama'a da dama, kuma dukiyarsu ta salwance.
Bisa rohoton da ofishin hedkwatar jagorancin ayyukan magance ambaliyar ruwa da kuma yaki da bala'in fari na kasar ya fitar, ya nuna cewa tun lokacin da aka shiga shekarar 2013, ya zuwa yanzu, gaba daya an samu birane da larduna 30 da suka gamu da bala'un ambaliyar ruwa da suka shafi mutane miliyan 47.7. Haka zalika rohoton ya bayyana cewa mutane 337 suka rasa rayukansu, mutane 213 suka bace da kuma lalacewar gidaje dubu 150. (Maryam)