Kwamitin kula da harkokin rage bala'i da ma'aikatar kula da harkokin jin dadin jama'a suna nan a kan shirin ko ta kwana
A ranar 23 ga wata, sashen kula da harkokin ceton mutane da rage bala'i na ma'aikatar kula da harkokin jin dadin jama'a ya ba da labari cewa, tun daga ranar 21 ga watan Yuli na bana, ambaliyar ruwa da aka samu a birnin Beijing sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 37, tare da bacewar wasu 7, kuma kwamitin kula da harkokin rage bala'i da ma'aikatar kula da harkokin jin dadin jama'a suna nan a kan shirin ko ta kwana.
Bala'in ambaliyar ruwa da aka samu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya daga ranar 21 ga wata, ya haddasa mutane kimanin dubu 120 da ke yankunan Fangshan, Tongzhou, Shi Jingshan da sauran yankuna 8 na birnin Beijing fadawa cikin tashin hankali na jin radadin bala'in, haka kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 37 a nan birnin Beijing, tare da bacewar wasu 7. (Bako)