Kungiyar ba da agaji ta Red Cross a kasar Kenya dake gabashin Afirka ta bayyana ranar Laraba cewa, a kalla mutane 32 sun rasa rayukansu, kana guda 18600 sun rasa muhallinsu bayan ambaliyar ruwa da ya auku sakamakon ruwan sama mai dimbin yawa.
Kungiyar ta Red Cross ta kuma ba da rahoton cewa, mutane 14 sun samu rauni, kuma har yanzu akwai mutane shida da ba'a gan su ba.
Sanarwa da kungiyar ba da agajin ta bayar na nunin cewa, ambaliyar ruwan ya shafi yankunan teku da yammacin kasar Kenya sakamakon karin saukar ruwan sama a yankin.
Gwamnati ta shawarci jama'a dake zama a wurare dake da yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa da su kaura zuwa kan tudu saboda yawan saukar ruwan sama a sassan kasar da dama.
Ambaliyar ruwan har wa yau ya yi sanadin lalacewar kadarori da kayayyakin more rayuwa a wurare da dama, kana ya kawo cikas kan harkoki kamar noma da ilmi.(Lami)