A ranar 15 ga wata, mataimakin firaministan Sin kuma mai ba da umurni, a hedkwatar ba da umurnin yaki da bala'in ambaliyar ruwa da na fari na kasar Wang Yang, ya shugabanci taro na cikakken zama na biyu, don gane da yaki da bala'in, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi a mayar da aikin yaki da ambaliyar ruwa gaban kome, don ba da tabbaci wajen ceton rayuwar mutane, da daidaita matakan da za a dauka, don rage hasarar da za a yi.
Wang Yang ya ce, ya zama dole sassa a matakai daban daban su sa ido, wajen gudanar da aikin hasashen yanayi, da maganin matsalolin da za a iya fuskanta, don ceton rayukan mutane, da yin kokarin warware matsalolin da ka iya aukuwa.(Bako)