Mugabe wanda yake mulkin kasar tun lokacin da ta samu 'yancin kanta a shekara ta 1980 ya zargi Ingila da kokarin ingiza wani juyin mulki a wannan zaben mai zuwa wanda yake kokarin sake samun nasara na wani shekaru 5 tsakanin shi da abokin hamayyarsa kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai a kan ragamar mulki.
Tsvangirai tsohon shugaban kungiyar kwadago na kasar, magoya bayan Shugaba Mugabe na masa kallon dan anshin shatan kasashen waje ne,
Shugaba Mugabe a yayin gangamim a garin Marondera, mai tazaran kilomita 70 ta gabashin Harare babban birnin kasar wanda kuma a nan ne Tsvangirai ya zaba don kaddamar da neman zabensa a makon da ya wuce, ya shaida wa magoya bayansa cewa ba za'a taba samun gwamnatin rikon kwarya kamar yadda Ingila take bukata ba a kasarsa, don haka kowa ya kalli lalurar gabansa su kyale kasar sa haka nan.
Ya yi bayanin cewa, a Zimbabwe dan Zimbabwe ne ya isa yayi mulkin kasar ba bare ba.
Mugabe dai a da shi dan lelen Ingila ne a farkon shekaru goma na mulkinsa inda suke mashi kallon Shugaba na Afrika dake da abin koyi sai dai amintakar ta lalace lokacin mulkin Tony Blair a matsayin Firaministan Ingila a game da wassu al'amurra da suka taso wadanda suka hada da biyan diyya da Ingila zata yi na gonakin da Turawanta suka mallaka kuma Gwamnatin Zimbabwe ta kwace bayan karban mulki daga hannun Ingila da ta masu mulkin mallaka. (Fatimah Jibril)