Gawar da aka gano baya bayan nan a arewacin kasar Mali za ta iyar kasancewa ta wannan dan kasar Faransa da kungiyar Al-Qaida reshen Maghreb wato AQMI ta sace a cikin watan Nuwamban shekarar 2011, a cewar wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa da aka fitar a ranar Lahadi.
Akwai alama sosai ta cewa tabbas gawar da aka gano ta kasance ta Philippe Verdon, in ji kakakin fadar Quai d'Orsay, Philippe Lalliot.
Haka kuma mista Lalliot ya bayyana cewa, "ana cigaba da gunadar da wasu karin bincike. Kuma muna cigaba da tuntubar iyalin wannan dan uwa namu domin basu duk wasu karin haske da muke da shi kan wannan al'amari. "
A cikin watan Maris, kungiyar AQMI ta sanar da kashe Philippe Vardon, da aka sace ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 2011 tare da wani bafaranshe guda. (Maman Ada)