Gong Jianzhong ya bayyana cewa, tun daga farkon watan Yuni a bana har zuwa yanzu, Sinawa fiye da dubu guda da suke haka zinariya ba bisa doka ba a kasar ta Ghana sun koma gida bisa taimakon da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Ghana yake bayarwa. Kana kuma gwamnatin Ghana ta ba da sauki a fannoni da dama, ta haka ana tafiyar da aikin janyewar Sinawan daga Ghana yadda ya kamata.
Mista Gong ya kara da cewa, gwamnatin Ghana ta sha bayyana cewa, hakar zinariya ba bisa doka ba yana gurbata muhallin kasar kwarai da gaske. Nan gaba za ta kara daukar tsauraran matakai a wannan fanni, za ta kuma yanke hukunci mai tsanani kan dukkan mutanen Ghana da na kasashen waje da ake tuhumarsu da laifin hakar zinariya ba bisa doka ba.
Haka zalika mista Gong ya sake yin kira ga Sinawan da suke hakar zinariya ba bisa doka ba da su fahimci halin da ake ciki, su fahimci muhimmanci batun da kuma illolin da aikace-aikacensu suka haifar, kana su daina dukkan abubuwan da suke yi ba bisa doka ba, su koma gida cikin hanzari, a kokarin magance kawo illa kan tsaron lafiyarsu da halaltattun hakkokinsu. (Tasallah)