A ranar 13 ga watan Yuni, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar da cewa, za a yi zaben shugaban kasar da na majalisar dokoki da na kananan hukumomin kasar a ranar 31 ga watan Yuli, amma shugaban jam'iyyar hamayya kuma firaministan gwamnatin hadaka Morgan Tsvangirai ya ki amincewa da wannan bisa hujjar cewa ba a shirya domin gudanar da zaben sosai ba. Sakamakon matsin lamba daga jam'iyyar hamayya da kuma kungiyar raya yankunan kudancin kasashen Afrika SADC, Mugabe ya amince da mika rokon jinkirtar da babban zaben ga babban kotun kasar.
Bayan da kotun ya musunta rokon, kakakin mista Tsvangirai ya bayyana cewa, shawarar da kotun koli ta yanke ita ce domin siyasa, amma za a yarda da sakamakon ba tare da ci gaba da kai kara ba.
A shekarar 2008, an samu rikici a babban zabe a kasar Zimbabwe, a karkashin shiga tsakani daga kungiyar SADC, an kafa gwamnatin hadaka a kasar. A watan Maris na bana, an zartas da sabon tsarin doka, bisa sakamakon jefa kuri'un raba gardama, kuma abin da ya kawar da shingaye game da babban zaben kasar.
A babban zaben da za a yi. Mugabe mai shekaru 89 da Tsvangirai mai shekaru 61 za su sake fafatawa.(Bako)