Le Drian ya ce, yawan sojojin kasar Faransa dake Mali zai ragu, zuwa kimanin 2000 a karshen watan Agusta, wato bayan an gama zaben shugaban kasar Mali wanda za'a yi a watan Yuli na bana. Ya zuwa karshen bana kuma, yawan sojojin Faransa dake Mali zai ragu zuwa kimanin 1000.
Le Drian ya kara da cewa, sojojin kasar Faransa kuwa yawancinsu suna hake a kewayen birnin Gao, babban birni na farko dake arewacin kasar Mali da kuma yankin Ifo Las, faffadan tsaunin dake arewa maso gabashin kasar Mali, wadanda suka taba yin yake-yake tare da kungiyoyin masu tsananin kishin addini da ta'addanci a yankin Ifo Las.
Yawan nauyin albarushin da sojojin Faransa suka kwace a maboyan masu tsattsauran ra'ayi ya kai ton 300,yayin da suke yin aikin soja a kasar Mali. (Zainab)