in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana tallafawa kasar Benin haka rijiya
2013-01-06 17:09:57 cri
A ranar Asabar 5 ga wata, aka kaddamar da aikin hakar rijiyoyi 100 a wani kauye dake dab da birnin Abomey Calavi a kudancin kasar Benin, aikin da ya kasance daya daga cikin tallafin da kasar Sin ke baiwa kasar Benin. Bikin ya samu halartar shugaban kasar Benin Boni Yayi, da ministan kasar mai kula da harkokin da suka shafi albarkatun kasa, makamashi, da kuma ruwa, Sacca Lafia da dai sauran manyan jami'an kasar.

A jawabin ministan Sacca Lafia, ya ce, gwamnatin na ta kokarin samar da ruwan sha a shekarun baya, kuma hakan ya fara amfanawa kashi 61% na al'ummar kasar a shekarar 2011 maimakon kashi 35% a baya a shekarar 2002. Bisa shirin gwamnatin, in ji shi, ana da niyyar kara wannan kaso zuwa 67% a shekarar 2015, sai dai ba za a samu damar cimma wannan buri ba, in babu abokan dake baiwa kasar Benin kudi da fasahohi ba tare da nuna son kai ba, kamar kasar Sin.

A cewar Mr. Lafia, gwamnatin kasar Benin da jama'arta suna godiya ga kasar Sin bisa ga babbar gudummowar da take bayarwa a fannin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar Benin, da kokarin habaka hadin gwiwar da ke tsakanin Benin da Sin. Haka kuma in ji shi, ana maraba da kasar Sin don ta kara shiga cikin kokarin kasar Benin na sarrafa albarkatun ruwa a nan gaba.

A nasa bangare, jakadan kasar Sin dake kasar Benin, Mista Tao Weiguang, ya ce, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan kokarin kasashen Afirka, ciki har da kasar Benin, na neman kyautata zaman rayuwar jama'arsu, don haka kasar Sin tana nuna musu goyon baya, musamman ma a fannonin gina kayayyakin more rayuwa, makamashi, aikin jinya, da kuma ilimi.

A cewar Jakada Tao, kasar Sin na son ci gaba da kokarin hada kai tare da gwamnatin kasar Benin, don taimakawa mata tinkarar kabubalen da za ta iya fuskanta yayin da take kokarin raya tattalin arzikinta.

An ce, wadannan rijiyoyi 100 za a gina su a wasu jihohi dake arewa da tsakiyar kasar Benin, inda aka fi fama da matsalar karancin ruwa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China