in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya amince da baiwa Benin dalar Amurka miliyan goma domin kyautata tsarin kiwon lafiya na kasar
2012-03-16 15:49:05 cri
A Alhamis ranar 15 ga wata, an bayar da sanarwar cewa, kwamitin zartarwa na bankin duniya ya amince da baiwa kasar Benin wani karin taimakon dalar Amurka miliyan goma kwatankwacin Sefa biliyan biyar domin karfafa ayyukan da tuni aka fara na matakin gudanar da 'aikin karfafa ingancin tsarin kiwaon lafiya wato (PRPSS)'.

An nuna cewa, tsarin aikin farko na PRPSS ya samu tallafi daga kungiyar kasa da kasa kan cigaba ta IDA da bankin duniya, wanda ya tashi zuwa jimillar dalar Amurka miliyan 33,8, a ciki, miliyan 11 suka fito daga asusun gungun masu bada tallafin kudi. An fara wannan aiki a shekarar 2011 bisa muhimman manufofin bada taimako ga bunkasa samar da ayyukan kiwon lafiya masu inganci ga lafiya uwa da jinjirinta a kasar Benin, da karfafa karin aikin hukuma na ministan kiwon lafiya.

A cewar wannan kundi, karin taimakon da ya samu amincewa a ranar Alhamis na da burin tallafawa wajen aiwatar da tsarin samar da kulawar kyauta ga masu fama da zazzabin cizon sauro na IGPECP a cikin asibitocin kasar da aka fara tun cikin watan Oktoban shekarar 2011 zuwa ga mata masu juna biyu da kuma yara 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China