Bisa tsarin wadannan yarjeniyoyi biyu, gaba daya jimillar kudin da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Benin ta cimma kudin Sefa biliyan 16.08 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 30.3 kuma kudaden sun hada da taimakon kudin kyauta kimanin Sefa biliyan 5 kwatankwacin dalar Amuka miliyan 9.5 da kuma wani bashin da babu ruwa na Sefa biliyan 11 kimanin dalar Amurka miliyan 20.6.
Wadannan yarjeniyoyi guda biyu da aka sanya wa hannu sun kasance daya daga cikin ayyukan da aka cimma dake aiwatar bisa ga niyyar da bangaren kasar Sin ya dauka da kuma bisa sakamakon shawarwari tsakanin shugabannin kasashen biyu in ji mista Tao.
Hakazalika ya bayyana batutuwan tsarin gina rijiyoyi 100 domin samar da ruwan sha, gina makarantar koyar da fasahohi da maganar sake gina hanyar mota daga Akassato zuwa Bohicon da gwamnatin kasar Sin ta dauki nauyin zuba kudin ginawa, kuma za a fara wadannan ayyuka kafin karshen wannan shekara. (Maman Ada)