A lokacin bikin kaddamar da aikin, an gabatar da bidiyon mutanen da suka samu wannan taimako domin fadakar al'ummar kasar kan matsalar dake janyo hankali ta nakasassu a kasar Benin. A wannan karo na biyu, kusan kudin Sefa miliyan 107 aka samu daga mutanen kasar. A yayin kaddamar da biki a ranar Alhamis, kusan kudin Sefa miliyan 2 aka tattara nan take. Taimakon da aka samu ya fito musammun ma daga kamfanonin wayar salula, hukumomin kasa da kasa da na gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu. (Maman Ada)