in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba cigaban da ake samu ta fuskar tattaunawa a siyasance a Guinea
2013-04-25 10:48:48 cri

A ranar Laraba 24 ga watan nan ne babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya bayyana gamsuwarsa ga ci gaban da ake samu ta fuskar tattaunawa a siyasance dake gudana a kasar Guinea (Conakiri), matakin da ya yi fatan cewa, zai kasance ginshikin wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Mr. Ban wanda ya yi wannan tsokaci cikin wata sanarwa da kakakinsa Martin Nesirky ya fitar, ya ce, ya dada gamsuwa da ci gaban da aka samu, sakamakon sanya hannu kan takardar yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, da 'yan adawa, da kuma tsagin fadar shugaban kasa da aka yi ran 23 ga watan nan.

Don haka, sanarwar ta bukaci dukkanin jam'iyyun siyasar kasar, da su kauracewa tada tarzoma, su kuma marawa shirin warware matsalolin kasar baya ta hanyoyin lumana da shawarwari.

Sanarwar ta kara da yabawa sanarwar da shugaban kasar Alpha Conde ya yi a ranar Laraba cewa, za a dauki dukkanin matakan da suka wajaba, domin gudanar zabe mai nagarta a kasar, ciki hadda shigar da masu ruwa da tsaki daga kasashen ketare.

A 'yan kwanakin baya ne dai shugaba Conde ya sanar da shirin gwamnatinsa, na gudanar da zaben 'yan majalissun dokokin kasar a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa, lamarin da ya sanya 'yan adawar kasar zarginsa, da sanya ranar zaben ba tare da tuntubar su ba.

Da ma dai bisa doka, ya wajaba a gudanar da zaben na 'yan majalissa ne, watanni 6 bayan zaben shugaban kasar da ya gabata a watan Nuwambar shekakar 2010, sai dai hakan ya faskara, sanadiyyar rashin cimma daidaito tsakanin jam'iyyun adawar kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China