in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun ba da lamuni na IMF da bankin duniya sun yafewa kasar Guinea bashin dalar Amurka biliyan 2.1
2012-09-27 10:19:43 cri

A ranar Laraba 26 ga wata, cibiyar samar da cigaban kasa da kasa ta babban bankin duniya IDA, da asusun ba da lamuni na IMF suka bayyana yafewa kasar Guinea bashin dalar Amurka biliyan 2.1. A cewar mai magana da yawun asusun bada lamuni na IMF, wannan mataki ya kawo raguwar bashin kasashen waje, dake wuyan kasashen yammacin Afirka da kaso 66 bisa dari.

Mr. Harry Snoek wanda shi ne jakadan bankin na ba da lamuni a kasar ta Guinea, ya ce, daukar wannan mataki ya biyo bayan cika sharudan yafe bashin da kasar ta Guinea ta yi, ciki har da batun cika ka'idojin habaka tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar, matakan da wakilan majalisun zartaswar bankunan biyu suka tantance su. Wannan dai mataki ya sanya kasar Guinea cikin tsarin yafiyar bashi ga kasashe matalauta na HIPC.

"Cika wadannan sharuda na shiga tsarin HIPC, wata gagarumar nasara ce ga kasar Guinea, wadda ke haskakawa duniya irin cigaban da kasar ta samu a fagagen tattalin arziki ga tsarin mulkin dimokuradiyya, biyowa bayan babban zaben kasar da ya gudana cikin watan Disamban shekarar 2010." a ma'anar kalaman Mr. Harry Snoek.

Bisa wannan tsari na yafiyar bashi dai ana sa ran bankin ba da lamuni na IMF, da bankin habaka tattakin arzikin nahiyar Afirka ne za su samar da kimanin kaso 70 na kudadan, yayin da ragowar bankunan cinikayya da na masu ruwa da tsaki za su dauki raguwar nauyin bashin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China