in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta gayyaci kasar Sin da ma sauran kasashe su nemi ayyukan samar da ababan more rayuwa
2013-07-18 10:24:46 cri
A ranar laraba,a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, aka kawo karshen taron Afirka na tsawon kwanaki biyu kan samar da ababan more rayuwa, inda aka bukaci kasar Sin da ma sauran kasashe, su zuba jari a fuskar bunkasa ababan more rayuwa a cikin nahiyar.

Taron ya samu halartar gwamnatoci, shugabannin kafofi masu zaman kansu, da shugabannin masana'antu a nahiyar Afirka.

Wakilan na Afirka sun amince cewar bunkasa ababan more rayuwa zai bunkasa tattalin arzikin Afirka tun da samar da su zai kawo sauki matuka a fuskar cinikayya da kuma sufurin kayayyaki tsakanin kasashen nahiyar.

A cikin rahotonsa, babban bankin duniya ya bayyana cewa akwai koma baya na a kalla dalar Amurka biliyan 93 kowace shekara a fuskar samar da ababan more rayuwa a nahiyar.

Da yake jawabi a yayin taron Ministan hukumomin gwamnati na kasar Afirka ta kudu Malusi Gigaba ya bayyana cewa ya dace kasar Sin da kuma kasashen kungiyar BRICS, wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta kudu, kana da nahiyar Afirkan kanta, su zamo kafofin samar da kudaden bunkasa ababan more rayuwa a nahiyar.

Ya ci gaba da cewa zuwa yanzu, kasar Sin ita ce ke kan gaba a fuskar cinikayya a Afirka wanda ya haura kashi daya cikin uku, tare da cewar tsarin kasar Sin ya taimaka a fuskar bunkasa ababan more rayuwa da zuba jari a kasashen Afirka da dama.(Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China