A ranar Asabar 9 ga watan Yulin nan da muke ciki ne aka bude bikin nunin kade-kade da wake-waken al'ummar kasashen Afrika karo na 9 a birnin Brazzavile na Jamhuriyar kasar Congo, bikin da ke da nufin bunkasa harkokin wake-wake da ma al'adun nahiyar ta Afirka.
Shugaban Jamhuriyar kasar Congo Denis Sassou Nguesso ne ya ayyana bude wannan biki. Ita ma a nata bangare, babbar daraktar hukumar UNESCO Irina Bokova, da take jawabi gaban mahalarta bikin na bana, jan hankalin mawaka daga nahiyar ta Afirka ta yi, domin su zage-damtse wajen bunkasa al'adun da nahiyar ta gada daga kaka-da-kakanni. Da yake gabatar da nasa jawabi ministan al'adu, da yawan shakatawa na kasar Congo Jean-Claude Gakosso, kira ya yi da a kare al'adun nahiyar Afirka daga gurbata, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar dimbin kalubalen dunkulewar duniya, da hadewar al'adu.
Kimanin mawaka 30 ne daga kasashe 12 aka gayyata bikin na bana, wanda kuma ake fatan kammalawa nan da ranar 19 ga wata. Cikin mawakan da suka halarci bikin da kasar ta Congo ke shiryawa bayan shekaru biyu-biyu akwai daga Faransa da Amurka, da 'yan kasar Afirka ta Kudu da kuma kasar Senegal. (Saminu)