in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakamakon gasar kwallon kafa ta zakarun nahiyar Afirka
2013-07-09 11:12:58 cri
Wannan shine jadawalin dake kunshe da sakamakon gasar kwallon kafa ta zakarun nahiyar Afirka, zagaye na daya da aka kammala a karshen makon da ya gabata.

A garin Sousse Morocco ta ci kasar Tunisia kwallo daya mai ban haushi

A kuma birnin Dakar itama Senegal ta jefawa Mauritania kwallo daya a zare

A Bamako kuwa kasar Mali ce ta lallasa Gunea da ci Uku da daya

Sai kuma Burkina Faso da ta jefawa Niger kwallo daya a zare a wasan da aka buga na birnin Ouagadougou.

Wasan Najeriya da Ivory Coast kuwa wanda aka buga a garin Kaduna, Nigeria ce ta lallasa Ivory Coast da ci 4 da nema.

Sai kuma wasan da aka buga a birnin Kinshasa, inda Janhuriyar dimokaradiyyar Congo ta ci Congo Brazzaville 2 da 1

A garin Bujumbura kuwa Burundi ce ta tashi kunnan doki da Sudan ci 1 da 1

A garin Yaounde na janhuriyar Camaru kuwa, an soke wasan Kamaru da Gabon, bayanda Hukumar kwallon kafa ta duniya ta hana kasar Kamarun buga wasa, a matsayin hukunci kan laifin shisshigi da karya dokokin wasa da ta yi.

Sanarwa: har ila yau rahotanni don gane da zagayen wasan na farko sun tabbatar da cewa kasashen Libiya da Ghana sun samu karabasar maki, bayanda kasahsen Algeria da Benin suka janye daga gasar.

Ana sa ran fara zagayen gasar na biyu ne tsakanin ranekun 12 zuwa ta 14 ga watan nan na Yuli, da kuma ranekun 26 zuwa 28 ga watan na Yuli. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China