in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya ce, kasarsa za ta inganta huldar da ke tsakaninta da Afirka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya
2013-06-30 16:56:42 cri
Ranar 29 ga wata, shugaba Barack Obama na kasar Amurka da ke ziyara a kasar Afirka ta Kudu ya bayyana a birnin Pretoria na kasar cewa, kasarsa na sa muhimmanci kan kasashen Afirka, za ta kuma kara inganta huldar da ke tsakaninta da su ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, ciki hadda kasar ta Afirka ta Kudu.

Bayan da mista Obama ya yi shawarwari da takwaransa na Afirka ta Kudu Jacob Zuma, sun gana da manema labaru tare, inda Obama ya ce, yanzu Afirka na samun farfadowa. Nufinsa na ziyartar Afirka a wannan karo shi ne raya cinikayya a tsakanin kasarsa da Afirka, da neman samun zarafin zuba jari don ba da taimako wajen raya Afirka, ta yadda ita kanta Amurka za ta ci gajiya.

A nasa jawabi, mista Zuma ya ce, kasarsa na sa muhimmanci ga raya huldar da ke tsakaninta da Amurka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, wanda shi ne manufar kasashen 2. Yana fatan Amurka za ta mayar da bunkasuwar Afirka a matsayin wata kyakkyawar dama, ta kuma kara zuba wa Afirka jari.

Har wa yau kuma, mista Zuma ya bai wa Amurka shawarar tsawaita wa'adin aiwatar da "dokar taimakawa Afirka wajen samun bunkasuwa da ba su dama", wadda wa'adin aikinta zai cika a shekarar 2015. Mista Obama ya yi na'am da shawararsa tare da nuna cewa, zai nemi amincewar majalisar dokokin kasar, sa'an nan zai yi wa kamfanonin Amurka bayani kan fifikon da ake nunawa a fannin zuba jari a Afirka ko kuma sayar da kayayyaki a Afirka.

Afirka ta Kudu, zango ne na biyu a ziyarar mista Obama a wannan karo, inda tuni wanda ya riga ya ziyarci kasar Senegal, zai kuma ziyarci kasar Tanzaniya bayan Afirka ta Kudun.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China