A kasuwanni 14 da aka yi nazarinsu a yankin Asiya da tekun Pasifik, ma'aunin CCI na babban yankin kasar Sin ya kai matsayi na uku, biye da na kasashen Indiya da Indonesiya.
Rahoton ya ce, bunkasuwar ma'aunin CCI na babban yankin kasar Sin ta bayyana ne a fannoni hudu, wato samun guraben aikin yi, makomar tattalin arziki, kudin shiga, da kuma ingancin rayuwa.(Fatima)