in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jimllar GDP ta kasar Sin za ta karu a kalla kashi 7 bisa dari, in ji masanan tattalin arziki
2013-07-16 18:03:28 cri

Da Safiyar yau 16 ga wata ne, cibiyar tattauna harkokin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin ta kira wani taro karo na 49 wanda a kan yi shi a ko wane wata, inda masana tattalin arziki da dama suka ba da bayyanai kan kididdigar da aka bayar kan halin tattalin arzikin kasar Sin na farkon rabin wannan shekara.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, jimillar alkaluman GDP na kasar Sin ya karu da kashi 7.6 cikin dari a farkon rabin shekarar bana, wanda a watanni biyar a jere ke nan saurin karuwar tattalin arziki ya yi kasa bisa hasashen da tsohuwar gwamnati ta yi wato kashi 8 bisa dari, tsohon mataimakin direktan kwamitin hada-hadar kudi da tattalin arziki na majalisar wakilan jama'ar Sin Mr He Keng ya nuna cewa,

"Rashin samun bunkasuwar bukatun cikin gida da na waje ne ya haddasa rashin saurin bunkasuwar tattalin arzikin, kuma manufar tattalin arziki da kudi da aka bullo da su ba su dace da halin da ake ciki ba, abin da ya tsananta matsalar hada-hadar kudin. Matsalar kudi da muke fuskanta a kwanakin baya wata alama ce ta gargadi. Sa'annan dogaro da jarin da aka zuba a cikin dogon lokaci domin neman samun karuwar GDP ya haifar da wasu matsaloli ciki hadda yawan kayayyaki da aka samar ya fi wadda ake bukata."

Kwanan baya, firaministan kasar Sin Le Keqiang ya jaddada wajibcin daidaita halin tattalin arzikin kasar, inda ya ce ya kamata ma'aunin karuwar tattalin arziki da yawan wadanda ke da aikin yi da dai sauransu ba su yi kasa da hasashe da aka yi a baya ba, kuma hauhawar farashi bai kamata ya haura adadin da aka yi tanadi ba. Muddin ana bukatar a tabbatar da daidaituwar tattalin arziki. A ganinsa, yawan karuwar jimillar GDP bai kamata ya yi kasa da kashi 7 bisa dari ba.

Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Sheng Laiyun ya nuna cewa, gwamnati ta yi shirin nuna sanyi jikin saurin karuwar tattalin arziki. Wasu kafofin yada labarai na kasashen ketare sun ce, sabbin shugabannin kasar Sin suna kokarin sauya hanyar da kasar take bi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, wato mai da hankali sosai kan bukatun cikin gida. Game da tsarin da aka bi a nan gaba na dogaro da jarin da aka zuba domin neman samun bunkasuwar GDP, a ganin Mr He, shi ne dalilin da ya tsananta tsarin tattalin arzikin.

Mataimakin shugaban kwalejin binciken tattalin arziki na Jami'ar Jama'ar kasar Sin Liu Yuanchun kuwa, ya bayyana cewa, abin da ya jawo hankalin mutane shi ne yawan kudin da mazauna birane da na kananan garuruwa suka samu a farkon rabin shekarar bana ya karu da kashi 6.5 cikin dari da kashi 9.2 cikin dari bi da bi, saurin karuwarsu ya ragu da kashi 3.2 bisa dari. Ya ce,

"Yawan kudin da aka samu ya ragu a cikin watanni biyu a jere, kuma yawansu ya karu da yawa, abin da zai taimaka ga sauran fannoni da suke da alaka da wannan, abin da ya tilasta mu zura ido kan shi."

Manazarcin ya yi nuni da cewa, shugabannin kasar sun taba bayyana cewa, jimillar GDP ba ta zama mizanin auna ingancin ayyukan da jami'ai za su yi ba, abin da ya aike da sakon cewa, za a yi garambawul kan tsare-tsare da yin kwaskwarima da kuma gaggauta sauya hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki. Mataimakin direktan kwamitin masana tattalin arziki na cibiyar tattauna harkokin tattalin arziki ta kasa da kasa ta kasar Sin Mr Liu Kegu ya ce, nuna sanyi jikin saurin karuwar tattalin arziki zai taimaka wajen yin garambawul da kwaskwarima, ya kamata, bangarori daban-daban su kara karfinsu na tinkarar sauyawar halin da ake ciki.

Masana da dama suna sa ran alheri ga makomar tattalin arzikin kasar Sin. Game da batun sabuwar hanyar samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da za a bi, Mr Liu Kegu ya ce,

"Sabuwar hanyar da za a bi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki tana kunshe da manyan ka'idoji hudu, wato dora muhimmanci kan samun bunkasuwa mai inganci cikin sauri. Da kuma kara saurin samar da kayayyaki. Sa'anan da rage bata makamashi da fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Har ma da tabbatar da ingancin kayayyaki da za a samar musamman ma ingancin abinci." (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China