in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi kira da a fidda cikakken tsarin yaki da ta'addanci a Afirka
2013-05-14 09:56:37 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci da a fidda wani cikakken tsarin yaki da ta'addanci a nahiyar Afirka, ta hanyar bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar dake nahiyar.

Wata sanarwa da jagorancin kwamitin ya fitar, ta kuma samu amincewar kwamitin mai kunshe da mambobi 15, yayin da ake tsaka da mahawara kan hanyoyin shawo kan wannan matsala, ta nuna takaicin yadda batun ayyukan ta'addanci ke ci gaba da yi wa zaman lafiya da tsaron nahiyar ta Afirka barazana.

Mambobin majalissar sun kuma bayyana damuwarsu, kan yadda hare-haren da kungiyoyi masu dauke da makamai ke aiwatarwa ke dada yaduwa a daukacin fadin nahiyar. Duba da wannan halin da ake ciki ne kwamitin ya ayyana bukatar inganta tattalin arziki, da samar da jagoranci nagari, da rage fatara, da yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu, a matsayin hanyoyin dakile ayyukan ta'addanci a nahiyar, da ma sauran yankunan duniya baki daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China