A cikin jawabinsa ga hukumomin yaki da ta'addanci da hana yaduwar makaman kare dangi da ke karkashin shugabancin kwamitin sulhu, shugaban kwamitin da aka kafa bisa kuduri na 1267 a shekarar 1999, da kuma na 1989 na shekarar 2011 kan kungiyar Al-Qaida, Gary Quinlan ya ce, ya dace a yi dukkan kokarin tabbatar da cewa, takunkumin da aka kafa ya yi amfani sosai wajen hana kungiyar al-Qaida da mukarrabanta yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
Matakan sun kunshi tabbatar da cewa, ana kara sabunta takunkumi kan kungiyar al-Qaida, kuma su zamo da inganci don a samu aiwatar da su.
Dangane kuma da batun kasar Mali da yankin Sahel, kwamitin ya dora takunkumi kan dukkan kungiyoyin dake da alaka da kungiyar al-Qaida, gami da shugabanninsu da ma sauran jama'ar dake da nasaba da su.
A kuma ranar Jumma'a har ila yau, kwamitin sulhu ya saurari rahoto daga shugaban kwamitin yaki da ta'addanci Mohammed Loulichki, inda ya bayyana cewa, za a yi wani taro na musamman da zai mai da hankali a kan kara bunkasa hadin gwiwa da ba da tallafi ga kasashen yankin Sahel domin a karfafa matsayinsu kan yaki da ta'addanci. (Lami Ali)