in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin za ta kara hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka a fannin rage abkuwar bala'in fari
2011-09-26 13:52:29 cri

A ranar 25 ga wata a nan birnin Beijing na kasar Sin, a yayin taron manyan jami'an kasashen Sin da Afirka da aka yi kan batun rage abkuwar bala'in fari, ministan ma'aikatar harkokin jama'ar kasar Sin Li Liguo ya nuna cewa, a halin yanzu, wasu kasashen Afirka suna fama da bala'in fari mai tsanani, a sanadin haka, gwamnatin kasar Sin za ta kara hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka a fannin rage abkuwar bala'in fari da ba da agaji ga kasashen dake fama da bala'in, ba ma kawai kasar Sin za ta samar da taimakon abinci ga kasashen Afirka dake fama da bala'in cikin gaggawa ba, har ma za ta more sakamakon yaki da bala'in fari da ta samu tare da kasashe daban daban na nahiyar Afirka, da haka, karfin rage abkuwar bala'in fari nasu zai kara karfuwa a kai a kai.

Ma'aikatar harkokin jama'ar kasar Sin da ofishin sakataren kula da harkar rage abkuwar bala'o'i na kasa da kasa na majalisar dinkin duniya sun shirya wannan taro tare.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, fari mai tsanani cikin dogon lokaci ya riga ya kawo babban tasiri ga bunkasuwar sha'anin noma na wasu kasashen Afirka. Tun bayan watan Maris na bana, kasashen dake kusurwar Afirka sun sake gamuwa da bala'in fari mai tsanani, jama'ar kasashen Kenya da Somaliya da Habasha da sauransu da yawansu ya kai sama da miliyan 10 suna fama da karancin abinci mai tsanani.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China